![]() |
|
2019-12-24 13:27:55 cri |
Jiya Litinin, sojin gwamnatin Somaliya sun yi musanyar wuta da masu tada kayar baya na kungiyar Al-shabaab a kudancin kasar, inda suka harbe mayakan kungiyar 8 har lahira. A nata bangaren kuwa, kungiyar ta ce, ta kashe sojojin gwamnati kasar su 8.
Kungiyar Al-shabaab na da alaka sosai da kungiyar Al-Qaeda, wadda ta dade take aiwatar da ayyukan ta'addanci a Somaliya, da masu wasu kasashe masu makwabtaka. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China