![]() |
|
2019-12-29 16:38:53 cri |
Kakakin gwamnatin kasar Somaliya ya bayyanawa 'yan jaridar kamfanin dillancin labaru na Xinhua a wannan rana da yamma cewa, yawan mutanen da suka mutu a sakamakon harin ya kai 79, tare da raunata mutane 149.
Shugaban kasar Somaliya Mohamed Abdullahi Farmajo ya yi Allah wadai da harin, tare da bayar da sanarwa cewa, wannan rana rana ce ta nuna juyayi. 'Yan ta'adda sun kai hari ga fararen hula, wato yara da iyalansu. Shi da iyalan mutanen da suka mutu dukkansu sun nuna juyayi sosai.
Mataimakin wakilin musaman na babban sakataren MDD Adam Abdelmoula shi ma ya yi Allah wadai da harin, ya ce MDD za ta ci gaba da nuna goyon baya ga jama'ar kasar Somaliya da gwamnatin kasar.
Harin bom ya fi tsanani ne da aka samu a kasar Somaliya tun baya watan Oktoba na shekarar 2017, babu wata kungiya ta sanar da dauka alhakin kai harin ba. (Zainab)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China