Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ta sake jin kunya a ranar kare hakkin bil Adama ta duniya
2019-12-10 20:35:54        cri

Yau 10 ga watan Disamba, rana ce ta kiyaye hakkin bil Adama ta duniya, Amurka wadda har kullum take mayar da kanta a matsayin mai kare hakkin bil Adama, ta sake jin kunya saboda MDD ta fitar da wani sabon rahoto, inda aka bayyana cewa, an kama yara 'yan ci rani da yawan gaske ba bisa ka'ida ba a Amurka.

Kafofin watsa labaran Amurka sun gabatar da rahotanni cewa, tun daga watan Disanban bara zuwa wannan lokaci, a kalla yara 'yan ci rani biyar wadanda ake tsare da su ne suka mutu, lamarin da ya nuna cewa, yanayin kiyaye hakkin bil Adama da Amurka ke ciki yana kara tsanani, kuma hakan ya shaida cewa, wasu 'yan siyasar Amurka ba su da kunya yayin da suke tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran kasashe.

Hakika lamarin bangare daya ne kawai a cikin al'amurran keta hakkin bil Adama a Amurka. A cikin wani rahoton da kwamitin yaki da nuna wariyar launin fata na MDD ya fitar, an bayyana cewa, Amurka ta dade tana nuna wariyar launin fata.

Wasu kafofin watsa labarai na Birtaniya su ma sun nuna cewa, ya zuwa watan Maris na bana, takardun dake shafar batun keta hakkin bil Adama a cikin Amurka da masu binciken batun kare hakkin bil Adama suka gabatar sun kai fannoni sama da 20, amma Amurka ta yi shiri kan wannan batun.

Abun da ya sa hankalin al'ummun kasashen duniya ya tashi shi ne, duk da cewa, yanayin kare hakkin bil Adama da Amurka ke ciki yana kara tsanani, amma Amurka ba ta daina zargin yanayin kare hakkin bil Adama da sauran kasashe ke ciki ba, har ta zartas da dokar kare hakkin bil Adama na Uygur ta shekarar 2019 a kwanakin baya, inda ya soki manufar kasar Sin kan yankin Xinjiang.

Don haka, duniya na fatan wasu 'yan siyasa na Amurka za su duba ainihin yanayin da kasarsu ke ciki, su daidaita matsalar da kasarsu take fuskanta, sannan su daina zargi sauran kasashe kamar yadda suke so.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China