Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta ce za'a bayyana sakamakon gwajin dabaru biyu na samar da magani ga masu fama da cutar COVID-19
2020-02-21 10:38:09        cri
Babban darektan hukumar lafiya ta duniya wato WHO, Mista Tedros Adhanom Ghebreyesus ya sanar da cewa, nan da sati uku masu zuwa, za'a bullo da sakamakon gwaji na wasu muhimman dabaru biyu da a yanzu haka ake amfani da su, domin kulawa da mutanen da suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19. Ya kuma tabbatar da cewa, akwai kwararru daga kasar Amurka a cikin rukunin kwararru da WHO ta tura zuwa kasar Sin don yin bincike.

A wajen taron manema labarai da aka shirya jiya a hedkwatar WHO dake Geneva, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce, dabarun biyu da WHO ke gudanar da gwajinsu, sun hada da hade magunguna biyu masu yaki da cutar AIDS, wato Lopinavir da Ritonavir, da kuma wani nau'in magani mai suna Remdesivir dake yakar sauran wasu kwayoyin cuta, wadanda ake sa ran za su taka rawa.

Rahotannin sun ce, a halin yanzu ana baiwa mutane wadannan magungunan a Wuhan domin gudanar da bincike.

Mista Tedros Adhanom Ghebreyesus ya kara da cewa, rukunin WHO dake kunshe da kwararru daga bangarorin ilimin annoba, da kwayoyin cuta, da kiwon lafiya daga kasashe daban-daban, na gudanar da ayyukansu a kasar Sin, wadanda ke hada kai da takwarorinsu na kasar domin lalibo bakin zaren daidaita yaduwar cutar.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China