Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta ce barkewar kwayar Cutar Corona ba ta shafi duk duniya ba
2020-02-05 10:38:03        cri

Hukumar lafiya ta Duniya WHO, ta ce barkewar kwayar cutar Corona ba ta zama annoba da ta shafi duk duniya ba, sai dai tana da kalubale da dama, tana mai cewa yaki da jita jita dangane da batun na da muhimmanci.

Daraktar sashen tunkarar cututtuka masu yaduwa na hukumar, Dr. Sylvie Briand ce ta bayyana hakan jiya a Geneva, inda ta ce WHO ta yi ammana barkewar cutar ba ta shafi duk duniya ba.

Ta ce dalilinta shi ne, kaso 78 na wadanda suka kamu da cutar kawo yanzu, sun fito ne daga lardin Hubei, wurin da cutar ta samo asali, inda take yaduwa daga mutum zuwa mutum. A wajen Hubei kuwa, akwai wanda suka kamu da cutar, sannan suka bar lardin zuwa wasu sassan kasar, kafin a hana shiga da fita a lardin. Inda ta ce makamancin wannan lamari aka samu a sauran kasashe 23 da aka tabbatar da an samu wadanda suka kamu da cutar.

Dr. Sylie Briand ta ce hukumomin kasar Sin sun dauki matakai dommin takaita yaduwar cutar a wajen Hubei, haka kuma suna ta gina asibitoci domin kula da mutane da rage mace-mace.

Har ila yau, ta ce dabarar da aka dauka yanzu haka a wajen Hubei da sauran kasashe ita ce, daukar matakan dakile yaduwar cutar domin gudun sake samun irin yayanin da ake ciki a Hubei, shi ya sa kasashe suka fara daukar matakan kebewa da kula da marasa lafiya da neman wadanda suka yi mu'amala da su tun da wuri.

Sai dai Dr. Briand ta ce jita jita ko kuma labaran kanzon kurege dake yawo, na iya illata matakan da aka dauka na yaki da cutar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China