Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagar kwararrun WHO za su ziyarci Sin game da batun yaki da annobar coronavirus
2020-02-11 11:02:05        cri
Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya (WHO), Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana da yammacin Lahadi cewa, tawagar kwararrun masanan kasa da kasa na hukumar WHO za su ziyarci kasar Sin domin bibiyar batun yaki da annobar novel coronavirus da ta barke.

Tedros ya wallafa a shafinsa a twita cewa, yana filin jirgin sama domin tabbatar da ganin mambobin babbar tawagar hukumar ta WHO wanda ta kunshe kwararrun masana kan batun annobar cutar sun ziyarci kasar Sin. Dr. Bruce Aylward, shi ne zai jagoranci tawagar, wanda ya kasance kwararren masanin cutuka masu saurin yaduwa da daukin gaggawa ne na kasar Kanada, kana kwararren masanin ayyukan gaggawa na kula da lafiyar al'umma.

Babban jami'in na WHO bai yi wani karin haske game da ayyukan da tawagar ta tsara gudanarwa ba.

Ya kara dacewa, babbar manufar tawagar ita ce domin neman karin ilmi daga takwararta ta kasar Sin bisa ga irin ayyukan da suke gudanarwar na dakile annobar domin duniya ta samu abin koyi daga kwararrun kasar Sin.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China