Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Ana fatan kwararrun Sin za su ba da taimako ga tsara shirin nazarin cutar coronavirus
2020-02-12 12:45:02        cri

Jiya Talata, an bude taron dandalin bincike da kirkire-kirkire kan cutar coronavirus na kasa da kasa na kwanaki biyu a birnin Geneva na kasar Switzerland, wasu jami'an hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO sun bayyana cewa, "muna maraba da kwararrun kasar Sin da su fito da tsarin nazarin cutar coronavirus, kuma muna fatan za su ba da muhimmiyar gudummawa a wannan aiki."

Babban sakataren WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyanawa taron manema labaran da aka yi a wannan rana cewa, kasar Sin tana da fasahohin fuskantar wannan cuta, muna fatan kwararrun kasar Sin za su ba da taimako na a zo a gani a aikin tsara shirin nazarin cutar corona virus.

Mataimakiyar babban sakataren hukumar WHO, kana shugabar dandalin taron tattaunawa na wannan karo Marie-Paule Kieny ta bayyana cewa, "kwararru na kasar Sin sun riga sun shiga cikin wannan taron, kuma tana fatan za su ci gaba da shiga a dama da su cikin aikin tsarawa da tabbatar da shirin nazarin cutar coronavirus."

Bugu da kari, babbar masaniyar hukumar WHO Soumya Swaminathan ta ce, likitoci guda biyu na cibiyar kandagarki da hana yaduwar cutar coronavirus ta kasar Sin sun halarci taro da ma gabatar da muhimman bayanan da abin ya shafa ta yanar gizo a wannan rana, inda suka bayyana matakan nazarin da kasar Sin ta kaddamar a halin yanzu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China