Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zazzabin Lassa ya kara halaka mutane hudu a tsakiyar Najeriya
2020-02-10 10:27:49        cri

Mahukuntan Najeriya sun tabbatar da cewa, an kara samun rahoton mutane 9 da suka kamu da zazzabin Lassa a kasar, baya ga mutane hudu da cutar ta halaka a jihar Kogi dake yankin tsakiyar kasar.

Masani kan yaduwar annoba a jihar ta Kogi Austin Ojotude, ya shaidawa manema labarai a Lokoja, babban birnin jihar cewa, cutar wadda Bera ke yada ta, ta barke a jihar ce kimanin wata guda da ya gabata.

Ojotude, ya bayyana cewa, alkaluman da jihar ta fitar sun nuna cewa, ya zuwa ranar Asabar, akwai mutane 31 da ake zaton sun kamu da cutar da kuma mutane 177 da suka yi mu'amula da wadanda suka kamu da cutar a jihar.

Cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya(NCDC) ta bayyana cewa, ya zuwa yanzu, yawan wadanda cutar ta halaka a baya-bayan a kasar ya karu zuwa 47, inda aka tabbatar mutane 365 sun kamu da cutar, wadda ke haddasa zazzabi mai tsanani ke ci gaba da yaduwa a kasar mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China