Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zazzabin Lassa ya halaka mutane 41 a Najeriya
2020-01-30 15:31:56        cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, mutane 41 ne aka tabbatar sun mutu, sakamakon barkewar zazzabin Lassa na baya-bayan nan a kasar, yayin da cutar ke ci gaba da yaduwa a kasar mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka.

Da take karin haske cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu a Abuja, fadar mulkin kasar, cibiyar yaki da cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa, daga farkon wannan shekara zuwa yanzu, an tabbatar da cewa, mutane 258 sun kamu da cutar a jihohi 19 cikin 36 na kasar. Ya zuwa yanzu akwai mutane 689 da ake zaton sun kamu cutar. Hukumar ta ce, galibi a jihohin Ebonyi da Edo da Ondo dake kudancin kasar.

Cibiyar NCDC ta bayyana cewa, ma'aikatan lafiya guda biyar na daga wadanda cutar ta halaka. Yanzu haka an kafa cibiyar kulawar gaggawa don taimakawa matakan yaki da cutar a fadin kasar.

A cewar ministan lafiyar Najeriya, mahukunta sun himmatu wajen ganin bayan wannan cuta, da sanya-ido da ma tuntubar wadanda suka kamu da cutar a jihohin da ta bulla.

Ya ce, Najeriya tana ba da gudummawa ga aikin binciken samar da maganin cutar zazzabin na Lassa, ta yadda za a kawo karshen cutar baki daya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China