Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nijeriya za ta kafa dakin gwaji na musammam na 6 domin yaki da zazzabin Lassa
2020-02-15 16:39:08        cri
Nijeriya na gab da kafa dakin gwaji na musammam da zai kara karfin kasar na gwajin cututtuka, yayin da take tsaka da fama da barkewar zazzabin Lassa tun a farkon shekarar nan.

Ministan lafiya na Najeriya Osagie Ehanire ya ce, dakin gwajin, zai zama irinsa na 6 da aka kafa musammam a cikin kasar domin gwajin zazzabin Lassa, mai haifar da matsanancin rashin lafiya dake iya yaduwa, da ya addabi sassan kasar.

Ministan ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa, idan aka kammala dakin gwajin, zai inganta karfin sauran dakunan gwaji 5 da ake da su wajen gwaje- gwajen samfuran gwaji a fadin kasar.

Yanzu haka, kasar ta yammacin Afrika na da dakunan gwaje-gwaje 5 a jihohin kudancin kasar da suka hada da Ebonyi da Lagos da Edo da Ondo da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Ministan ya yi bayanin cewa, bisa taimakon hukumar lafiya ta yammacin Afrika WAHO, za a kafa sabon dakin gwajin ta yadda ba za a sha wahalar kai samfuran gwaje gwaje ba, kamar dai yadda aka yi la'akari da wannan batu yayin kafa sauran dakunan gwaje-gwaje a fadin kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China