Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta tanaji dala dubu 98.3 ga duk wanda ya gano maganin cutar coronavirus da zazzabin Lassa
2020-02-14 21:06:24        cri
Ministan ma'aikatar kimiyya da fasaha a Najeriya Dr. Ogbonnaya Onu, ya ce gwamnatin kasar za ta ba da ladan kudi har naira miliyan 36, kwatankwacin dalar Amurka 98,372, ga duk wani dan kasar da ya yi nasarar gano maganin cutar coronavirus da zazzabin Lassa.

Ministan ya gabatar da wannan kalubale ne a jiya Alhamis, yayin liyafar kammala aiki, da aka shiryawa tsohon daraktan binciken fasahar sinadarai karkashin ma'aikatar kimiyya da fasahar. Dr. Ogbonnaya Onu ya ce hakan wani kalubale ne ga masana kimiyyar kasar.

Ya ce " Ba wani abu da zai gagare mu muddin dai mun daura damarar yin sa, kuma Najeriya za ta ci gaba da ba da gudummawa, ga bukatun al'ummar duniya."

Ministan ya ce ladan da aka tanada na naira miliyan 36, tamkar kaimi ne ga masu binciken kimiyya na kasar, domin su kara kwazo a fannin kirkire kirkire, Daga nan sai ya jaddada kudurin gwamnatin Najeriya, na ci gaba da mara baya ga ayyukan bincike da samar da ci gaba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China