Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta cimma nasarar harbar taurarin dan Adam guda 4
2020-02-20 11:32:12        cri

Da misalin karfe 5 da minti 7 na safiyar yau Alhamis, kasar Sin ta cimma nasarar harba taurarin dan Adam na gwaji guda hudu, ciki har da tauraron C, da tauraron D, da tauraron E da kuma tauraron F.

An harba wadannan taurarin dan Adam na gwaji da rokar dako ta Changzheng samfurin D mai lamba 2, a cibiyar harba taurarin dan Adam ta birnin Xichang, kuma dukkansu sun shiga hanyar su bisa hasashen da aka yi, yayin da aka kammala ayyukansu cikin nasara. An gudanar da wannan gwaji ne domin raya sabbin fasahohin bincike kan duniyarmu.

Bugu da kari, kwalejin nazarin fasahohin jiragen sama ta birnin Shanghai, ta sarrafa rokar dako ta Changzheng samfurin D mai lamba 2, da taurarin dan Adam na gwaji na C da D, sa'an nan kuma, jami'ar masana'antu ta birnin Harbin ta sarrafa tauraron dan Adam na E, yayin da kamfanin taurarin dan Adam na Dongfanghong ya sarrafa tauraron dan Adam na F.

Kuma wannan shi ne aikin harbawa karo na 326 da rokokin dako samfurin Changzheng suka gudanar. (Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China