Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta harba tauraron dan Adam na kasar Habasha
2019-12-20 19:29:36        cri
A yau Juma'a ne kasar Sin ta harba tauraron dan Adam da ta mallakawa kasar Habasha zuwa sararin samaniya, tauraron da ake sa ran zai taimakawa Habashan wajen gudanar da binciken yanayi. Shi ne kuma tauraron dan Adam na farko da Habashan ta mallaka.

An harba tauraron ne dai da rokar harba taurarin dan Adama ta Long March-4B, tare da wasu taurarin guda 8, daga tashar harba kumbuna dake Taiyuan, na lardin Shanxi dake arewacin kasar Sin. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China