Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta kaddamar da na'urar harba tauraron dan adam samfurin Long March-5
2019-12-21 15:20:47        cri
Kasar Sin tana shirin kaddamar da na'urar harba tauraron dan adam karo na uku samfurin Long March-5, wanda ita ce na'urar dake dauke da tauraron dan adam mafi girma ta kasar Sin, tun a yau Asabar an riga an kai na'urar zuwa cibiyar da ake harba tauraron dan adam dake Wenchang a lardin Hainan dake shiyyar kudancin kasar Sin.

Na'urar, samfurin Long March-5 Y3, an shirya kaddamar da ita ne a karshen watan Disamba, kamar yadda hukumar dake lura da sararin samaniyar kasar Sin ta sanar.

Shirin harba na'urar na Long March-5 na daga cikin muhimmin aikin sararin samaniyar kasar Sin a wannan shekarar, kasancewa ita ce mafi girma, hakan ya kara tabbatar da ingantuwar makomar shirin ayyukan sararin samaniyar kasar Sin.

Idan shirin ya samu nasara, na'urar za ta gudanar da aikin harba tauraron zuwa duniyar Mars na farko na kasar Sin da kuma aikin harba tauraron dan Adam na Chang'e-5 zuwa duniyar wata domin samu wasu bayanai daga duniyar watan wadanda za'a kawo samfurinsu zuwa wannan duniya da muke ciki. Bugu da kari, sauya fasalin na'urar Long March-5B, za'a iya amfani da shi wajen gina tashar ayyukan sararin samaniyar kasar Sin.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China