Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta kaddamar da jirgin ruwan binciken yankin kurewar duniya Xuelong-2
2019-10-16 10:25:26        cri

Kasar Sin ta kammala kera jirgin ruwan binciken cikin teku kirar cikin gida irinta ta farko mai suna Xuelong-2, ko kuma Snow Dragon 2, don aikin binciken yankin kurewar kudancin duniya da kasar ke gudanarwa a karo na 36, wanda ta tashi daga birnin Shenzhen da yammacin ranar Talata.

Jirgin ruwan Xuelong shi ma zai shiga aikin, inda a karon farko wadannan jiragen biyu za su gudanar da aiki tare karkashin shirin binciken yankin kurewar kudancin duniya na kasar Sin.

Xuelong 2 zai bi ta tashar ruwan Zhongshan kafin daga bisani ta fara aikin bincike a tekun Cosmonauts da kuma babbar tashar nazarin kimiyya ta babbar ganuwa ta kasar Sin. Ana sa ran za ta kammala binciken a karshen watan Maris na shekarar 2020.

Tawagar ta kunshi mambobi 413 wadanda za su gudanar da aikin binciken teku, da yanayi, da kankara, da kuma halittu. Haka zalika za su gudanar da aikin share fage domin gina tashar binciken kasar Sin ta biyar a yankin, kamar yadda daraktan cibiyar kula da aikin binciken yankunan kurewar duniya ta kasar Sin Qin Weijia, ya bayyana.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China