Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya aike da sakon taya murnar bude dandalin Zhongguancun na shekarar 2019
2019-10-17 19:42:02        cri

A yau ne, aka gudanar da taron dandalin Zhongguancun na shekarar 2019 a nan birnin Beijing, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sako don murnar bude taron.

A cikin sakonsa, Xi Jinping ya ce, a halin yanzu, ana fuskantar wani sabon juyin juya halin kimiya da fasaha da farfadowar masana'antu, abin da duniya ta sanya a gaba, shi ne neman raya ayyukan kirkire-kirkire, hadin kai da cin moriya tare. Sin na fatan kara hadin kai da kasashen duniya da more ci gaban da Sin take samu a fannin kirkire-kirkire, da kuma raya kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya da sauran kasashe. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China