Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kara jiragen kasa na musamman don dawo da maaikata bakin aiki
2020-02-20 10:53:59        cri

Domin baiwa fasinjoji wadanda za su komo ayyukansu damar yin hakan cikin sauri kuma lami lafiya, gwamnatocin wurare daban daban, da hukumomin jiragen kasa na kasar Sin, sun himantu wajen cimma matsaya, da kara jiragen kasa na musamman, don biyan bukatun dawo da ma'aikata wuraren aiki.

Da safiyar ranar 19 ga wata, jirgin kasa na musamman na farko da aka bude, don biyan bukatun gwamnatocin lardunan Guangdong da Guangxi, ya tashi daga tashar Baise ta lardin Guangxi zuwa yankin delta na kogin Zhuangjiang.

Hukumomin jiragen kasa sun tura wasu ma'aikatan musamman, don jarogantar ma'aikata masu komawa ayyukansu wajen yin rajista, yayin da tashoshin jiragen kasa ma sun kara aikin kandagarki, da shawo kan cutar numfashi ta COVID-19, har ma sun gudanar da ayyukan kashe kwayoyin cuta a muhimman wuraren dake tashar, ciki har da hanyoyi, da yankin tashar jiran jirgi, da bayan gida da dai sauransu.

A yankin delta na kogin Yantse mai ci gaban tattalin arziki kuwa, hukumomin jiragen kasa na birnin Shanghai, sun samar da jiragen kasa na musamman har 5 daya bayan daya, domin taimakawa ma'aikatan dake sauran wurare su koma wurin aiki cikin sauri. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China