Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na kokarin ingiza kamfanoni da su dawo bakin aikinsu
2020-02-19 17:12:39        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a yau Laraba cewa, a halin yauzu, Sin na samun ci gaba mai armashi, saboda matakan tinkara, da kandagarkin cutar numfashi ta COVID 19 da ta dauka, kuma tana yin iyakacin kokarin ingiza kamfanoni daban-daban su dawo bakin aikinsu, ciki hadda daukar matakin daidaita matsalolin da kamfanoni masu jarin ketare ke fuskanta, ta fuskar zuba jari da samar da kayayyaki, da kuma gudanar da ayyukansu, don kawar da illar da cutar ta kawo musu. Tuni kuma wasu kamfanoni masu jarin ketare sun riga sun farfado da ayyukansu.

Geng Shang ya ce, a takaice dai, illar da cutar ta kawowa tattalin arzikin kasar Sin, ba za ta dore cikin dogon lokaci ba, kana gwamnatin kasar Sin na da ingantattun manufofin na ingiza tattalin arzikinta, kana burin samun bunkasuwar tattalin arziki a cikin dogon lokaci a kasar Sin ba zai canja ba. Jami'in ya ce Sin na da niyyar cimma muradunta, na raya al'umma da tattalin arzikinta. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China