Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya aike da sakon ta'aziyya ga wadanda annobar coronavirus ta kashe
2020-02-11 09:38:54        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping kana babban sakataren kwamitin tsakiyar Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin (CPC), a jiya Litinin ya aike da sakon ta'aziyyar mutanen da suka mutu a sanadiyyar annobar novel coronavirus kuma ya jajantawa iyalan wadanda annobar ta hallaka bisa hakuri da juriyar da suka nuna.

Xi, shugaban kasar Sin kana shugaban kwamitin koli na rundunar sojojin kasar Sin, ya kuma bayyana jimami ga majinyata da suka kamu da cutar kana da jajantawa iyalansu.

A madadin kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin CPC, Xi ya aike da sakon ta'aziyya da jajantawar ne a lokacin babban taron da aka gudanar ta hanyar bidiyo a asibitin Beijing Ditan tare da jami'an lafiyar dake ayyukan yaki da annobar cutar a lardin Hubei.

Xi ya nuna fatan alheri ga mambobin jam'iyya, da jami'ai, da kuma al'ummar Hubei, kana ya bayyana godiyarsa ga ma'aikatan lafiya, da jami'ai da kuma dakarun sojoji, da kuma dukkan masu ruwa da tsaki sakamakon sadaukar da kai wajen yaki da annobar cutar ta hanyar kandagarki da kuma shawo kan annobar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China