Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Syria da mayakan Kurdawa sun hada kai don yakar 'yan tawayen dake samun goyon bayan Turkiyya
2019-11-08 11:06:04        cri
Hukumar dake sanya ido a yakin Syria ta ce sojojin Syria da mayakan Kurdawa sun yi hadin gwiwa a ranar Alhamis, inda suka kwace kauyen dake karkashin ikon 'yan tawayen dake samun goyon bayan Turkiyya a arewacin Syria, a wani al'amaru dake nuna hadin gwiwa tsakanin dakarun bangarorin biyu da nufin fattatakar dakarun dake samun goyon bayan sojojin Turkiyya a arewacin kasar Syria.

A cewar hukumar sanya ido don tabbatar da kare hakkin bil adama a Syria, sojojin Syria da mayakan Kurdawan karkashin jagorancin dakarun (SDF) sun yi nasarar kwace ikon kauyen Um Shaifeh dake shiyyar lardin Hasakah bayan mummunar arangamar da aka yi tsakanin sojojin Turkiyya da 'yan tawayen dake samun goyon bayan Turkiyyar.

An cimma wasu yarjejeniyoyi ne tun a ranar 9 ga watan Oktoba karkashin jagorancin masu shiga tsakani na Rasha, lamarin da yayi sanadiyyar tsakaita yaki a wasu yankunan kasar, kuma ya baiwa dakaru sojojin Syria damar shiga yankunan dake karkashinn ikon Kurdawa dake kan iyakan Syria da Turkiyya domin dakatar da aniyar Turkiyyar na cigaba da yin lugudan wuta a yankin. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China