Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kaddamar da kwamitin kundin tsarin mulkin Syria a Geneva
2019-10-31 11:34:37        cri

A jiya Laraba ne aka kaddamar da kwamitin tsara kundin mulkin kasar Syria a birnin Geneva. Kwamitin dai na kunshe da mambobi hamsin-hamsin daga bangaren 'yan adawa, da kungiyoyin al'umma da kuma wakilan gwamnati.

Wakilin musamman na MDD a Syria Geir Pedersen, tare da jagororin kwamitin Ahmad Kuzbari daga bangaren gwamnati, da kuma Hadi Albahra daga bangaren 'yan adawa ne suka shugabanci kaddamar da kwamitin, yayin bikin da ya samu halartar jimillar mambobinsa 150, wadanda suka yi zaman farko cikin helkwatar MDD dake Geneva.

Wakilin na MDD ya shaidawa mambobin kwamitin cewa, ganin yadda dukkanin sassa suka nuna kyakkyawar niyyar su tun da fari, hakan na tabbatar da fatan da ake da shi na samar da managarcin yanayin aiki tsakanin su.

Jami'in ya kara da cewa, aikin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar, shi ne matakin farko na kawar da wahalhalun da al'ummar Syria suka fuskanta, kasancewar kundin tsarin mulkin kasar na kunshe da kudurorin kare 'yancin 'yan kasa, da na bunkasa yanayin siyasa, da al'adu, da na zamantakewa da tattalin arziki, da tabbatar da dokoki da kuma jagoranci na gari. An amince da kafa wannan kwamiti ne a birnin Sochi na kasar Rasha cikin watan Janairun shekarar 2018. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China