Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin a Nijeriya ya fidda sharhi mai taken "Sin ta dauki matakai masu amfani a kan lokaci wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19"
2020-02-18 11:30:22        cri

Jiya Litinin, wasu manyan kafofin watsa labarai na kasar Nijeriya, ciki har da jaridar The Leadership, sun gabatar da sharhin da jakadan kasar Sin dake kasar Nijeriya Zhou Pingjian ya rubuta, mai taken "Kasar Sin ta dauki nauyin ta, ta kuma fidda matakai masu amfani a kan lokaci domin yaki da cutar numfashi ta COVID-19".

Bayan bullar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Sin, kasar ta yi kira ga dukkanin al'ummomin kasar da su yi yaki da cutar. Kana, gwamnatin kasar ta dauki matakai mafi karfi, kuma mafi amfani domin hana yaduwar cutar, har ma matakan sun wuce yadda hukumar lafiya ta duniya WHO ke bukata, da wasu matakan da aka kayyade cikin manufofin kiwon lafiyar kasa da kasa. Yanzu, Sin ta cimma nasarori da dama ta fuskar hana yaduwar cutar numfashi bisa iyakacin kokarin da ta yi.

A nan gaba kuma, kasar Sin za ta ci gaba da karfafa hadin gwiwarta da sauran kasashen duniya ba tare da boye komai ba, domin kare zaman lafiyar yankin da ta kasa da kasa. Kuma, kasar Sin za ta kula da 'yan kasashen waje dake kasar kamar yadda take kulawa da jama'arta. Kasar Sin tana son yin mu'amala da Nijeirya kan duk wani sabon labarai game da cutar, kuma za ta yi kokarin kare lafiyar 'yan kasar Nijeriya dake kasar Sin, da ma tsaron dukkanin al'ummomin Sin da Nijeriya.

A 'yan kwanakin nan, gwamnati da al'ummomin Nijeriya, sun nuna babban goyon baya ga kasar Sin wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19, kuma kasar Sin tana godiya sosai. Kasar Sin ba za ta manta da taimako da goyon bayan da sauran kasashen duniya suka yi mata a lokacin da take cikin mawuyacin hali ba. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China