Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta yabawa matakan da Sin ke dauka wajen dakile annoba
2020-02-04 09:47:03        cri
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) a jiya Litinin ta yabawa kwararan matakan da kasar Sin ke dauka wajen shawo kan annobar cutar numfashi ta coronavirus da ta barke, inda ta bukaci dukkan kasashen duniya da su dauki kwararan matakan dakile cutar, domin kaucewa yaduwarta, a maimakon tsoron barkewarta kawai.

Da yake jawabi a lokacin babban taron manyan jami'an hukumar ta WHO karo na 146 wanda aka bude a ranar Litinin, darakta janar na hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce, kasar Sin ta dauki tsauraran matakai a yankin da cutar ta barke, da kuma tushen annobar, wanda a cewarsa matakin ba kawai ya baiwa Sinawa kariya ba ne, har ma ya taimaka wajen takaita bazuwar kwayoyin cutar zuwa sauran kasashen duniya.

Ya ce, ba don wadannan dabaru da kasar Sin ta yi amfani da su ba, to da yawan mutanen da za su kamu da cutar a wajen kasar Sin ya ninka wanda aka samu a halin yanzu.

Tedros ya ce, kawo yanzu, mutane 146 aka tabbatar da sun kamu da cutar a kasashen duniya 23 ban da kasar Sin. "Hakika adadin ba shi da yawa, kuma ba ya karuwa cikin sauri, don haka za'a iya shawo kan matsalar" in ji Tedros.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China