Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan harkokin wajen Sin ya yi kira kan hadin gwiwar bangarori daban daban a taron tsaro na Munich
2020-02-16 16:36:31        cri

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gabatar da jawabi a babban taron tsaro a Munich, inda ya bukaci dukkan kasashen gabashi da yammacin duniya da su kawar da duk wasu banbance banance dake tsakani kuma su rungumi tsarin hadin gwiwar bangarori daban daban.

Cikin jawabinsa, Wang ya yiwa mahalarta taron cikakken bayani game da halin da kasar Sin ke ciki a yanzu game da ayyukan yaki da annobar cutar numfashi ta novel coronavirus karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping na kasar.

Babban jami'in diflomasiyyar ya ce, tsauraran matakan da gwamnatin kasar Sin ke ci gaba da dauka suna haifar da kyakkyawan sakamako, kasar Sin tana da cikakken kwarin gwiwa ganin bayan annobar a yakin da take da cutar.

Ya kara da cewa, annobar da ta barke ta kara bayyanawa bil Adama cewa, batun da ya shafi shiyya yana iya sauyawa zuwa batu na duniya baki daya. Don haka, babu wata kasa a duniya da za ta iya kaucewa fuskantar barazana.

Wang ya bayyana wasu shawarwari hudu game da batun hadin gwiwar bangarori daban daban. Na farko, ya kamata kasashen duniya su amince da tsarin hadin gwiwar bangarori daban daban domin neman ci gaba tare. Tsarin hadin gwiwar bangarori daban daban bai lamincewa baiwa wata kasa daya tilo fifiko ba, a maimakon hakan, tsarin ya nuna cewa dukkan kasashen duniya suna da hakki iri daya don neman ci gaba tare.

Na biyu, ya kamata manyan kasashen duniya su aiwatar da abubuwan da suke furtawa idan ana batun maganar hadin gwiwar bangarori daban daban. Samun nasarar hadin gwiwar bangarori daban daban ya dogara ne kan irin rawar da manyan kasashe ke takawa da kuma sauke nauyin dake bisa wuyansu.

Na uku, kamata ya yi a kiyaye dokokin kasa da kasa idan ana batun hadin gwiwar bangarori daban daban. Ya ce hadin gwiwar bangarori daban daban bai yarda da ra'ayin kashin kai na kasa guda ba, tilas ne hadin gwiwar bangarori daban daban ya kasance bisa tsarin siyasar dangantakar kasashen duniya kuma tilas ne ya dace da dokokin kasa da kasa da adalci a tsakanin kasashen duniya.

Na hudu, ya kamata a kara fadakar da al'umma game da alfanun dake tattare da rungumar tsarin hadin gwiwar bangarori daban daban.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China