Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan harkokin wajen Sin zai tashi zuwa Jamus domin halartar taro game da tsaro
2020-02-12 19:57:43        cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi zai tashi zuwa kasar Jamus, domin halartar taron birnin Munich karo na 56, zai kuma jagoranci taro na 5 tare da ministan wajen Jamus Heiko Maas, a taron da zai maida hankali ga tattaunawa batutuwa da suka shafi kasashen biyu a fannin diflomasiyya da tsaro.

Da yake karin haske game da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Geng Shuang, ya ce za a gudanar da tarukan ne a ranekun Alhamis zuwa Asabar mai zuwa.

A cewar Geng Shuang, ministan wajen Jamus Heiko Maas, da shugaban taron tsaro na birnin Munich Wolfgang Ischinger ne suka gayyaci Mr. Wang Yi. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China