Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: Sin da Rasha na bada babbar gudunmawa wajen kiyaye zaman lafiya a duniya
2020-01-21 11:10:14        cri

Mamban majalisar gudanarwa kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya zanta da manema labarai a taron liyafar murnar sabuwar shekara ta 2020 da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta shirya a jiya Litinin, inda ya nuna cewa, bara an cika shekaru 70 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da Rasha, karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu, bangarorin biyu sun shiga wani sabon zamani dake hada kansu da taimakawa juna, da zurafafa tuntubar juna da yin kirkire-kirkire da neman amfanar juna da cin moriya tare, wadanda suke bada babbar gudunmawa wajen kiyaye zaman lafiya da karkon duniya.

Yayin da ya yi tsokaci kan dangantakar Sin da Amurka, ya ce, bara ta cika shekaru 40 da kafuwar dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, dangantakar kasashen biyu na shiga wani sabon mataki mai muhimmanci a tarihi, inda kuma ana fuskantar sauye-sauye da kalubaloli da dama. Ya ce, Sin na tsayawa kan kiyaye muradunta da suka dace, da kuma fatan yin shawarwari da Amurka bisa ka'idar zaman daidaito da mutunta juna, da cimma matsaya daya da kuma sa hannu kan yarjejeniyar tattalin arziki da ciniki a matakin farko, lamarin da ba ma kawai ya dace da moriyar jama'ar kasashen biyu ba ne, har ma ya samu maraba daga al'umomin duniya baki daya.

Yayin da ya tabo maganar shawarar "Ziri daya da hanya daya", Wang Yi ya nuna cewa, Sin ta cimma nasarar gudanar da taron kolin dandalin kasa da kasa kan shawarar karo na biyu a shekarar bara, inda aka cimma nasarorin hadin gwiwa har 283, da kuma sanar da kafa dangantakar abota da tuntubar juna tsakanin kasa da kasa. Ya kara da cewa, a wannan shekara dai karin kasashe 16 da kungiyoyin duniya sun shiga wannan shawara, hakan yasa yawan takardun hadin kai da aka kulla ya kai fiye da 200. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China