Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi ya yi shawarwari da takwaransa na Thailand
2020-02-05 13:30:35        cri

Jiya Talata, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya zanta ta wayar tarho da takwaran sa na kasar Thailand Don Pramudwinai.

Wang Yi ya nuna godiya ga Thailand, dangane da goyon baya da ta baiwa kasar Sin, da kayayyayin da ta samarwa Sin. Ya ce, kasar Sin da kasar Thailand sun zama 'yan uwan juna, suna kuma samarwa juna taimakon da ake bukata, a duk lokacin da wata ta shiga halin matsi. Ya ce kasar Sin da kasar Thailand suna da zumunci mai danko, kuma Sin za ta kiyaye lafiyar 'yan kasar Thailand dake zaune a Sin, kamar yadda take kiyaye al'ummomin ta.

Wang Yi ya ce, yanzu haka an fara cimma nasarori bisa kokarin da ake yi na yaki da cutar, kuma adadin rasuwar mutane sakamakon wannan cuta bai kai kaso 2.1% ba, wannan adadi bai kai adadin rasuwar mutane sakamakon sauran miyagun cututtuka a kasashen duniya ba. Kaza lika adadin mutanen da suka warke ya fi adadin rasuwar da aka samu, kana saurin karuwar mutane masu dauke da cutar yana raguwa. Ya ce kasar Sin tana da karfi, da Imanin cimma nasarar yaki da cutar. Kuma za ta habaka hadin gwiwar harkokin kiwon lafiya na kasa da kasa,bisa ka'idojin adalci, ba tare da boye komai ba.

A nasa bangare kuma, Don Pramudwinai ya bayyana goyon bayan Thailand ga kasar Sin, wajen yaki da cutar numfashi, ya kuma jaddada cewa, a wannan mawuyacin halin da ake ciki, kasar Thailand za ta kasance tare da al'ummomin Sin, kuma yana da imanin cewa, tabbas kasar Sin za ta cimma nasarar yaki da cutar numfashi cikin sauri, da kuma kwantar da hankulan al'ummar kasa.

Bugu da kari, kasar Thailand tana fatan samar da dukkanin taimakon da kasar Sin take bukata. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China