![]() |
|
2020-01-19 17:00:28 cri |
Wang Yi ya bayyana cewa, bangarori daban daban na kasar Myanmar sun nuna yabo ga ziyarar aikin, sun yi tsammani cewa, a yayin da ake cika shekaru 70 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Myanmar da Sin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki a kasar ta Myanmar, wadda ta kansance kasa ta farko da ya kai ziyara a sabuwar shekara, wannan ya shaida cewa, an sada zumunta a tsakanin kasashen biyu mai zurfi, da kuma bude sabon babi a wannan fanni. Kafofin watsa labaru na kasa da kasa sun kara maida hankali ga ziyarar aikin, sun yi tsammani cewa, aikin diplomasiyya da shugaban kasar Sin ya yi ya taimakawa sada zumunta a tsakanin Sin da Myanmar zuwa sabon matsayi, kana an samu babban ci gaba kan raya shawarar "ziri daya da hanya daya", ta hakan za a kara inganta tasirin Sin da aka kawo wa duniya baki daya.
Wang Yi ya kara da cewa, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin ta tsaya tsayin daka kan manufar samun bunkasuwa cikin lumana, da kaucewa yin kama karya da tsoma baki kan harkokin cikin gida na sauran kasashe, Sin za ta ci gaba da yin magana domin nuna goyon baya ga kasashe masu tasowa a duniya. Sin ta nuna goyon baya ga kasar Myanmar da ta ci gaba da bin hanyar da ta zaba, da tabbatar da moriyarta da girmamawarta a dandalin duniya. Sin ta girmama ikon mallaka da burin kasar Myanmar, da taimakawa wajen sa kaimi ga samun zaman lafiya da sulhuntawar al'ummar kasar Myanmar. (Zainab)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China