Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta bayyana kudirinta na tattaunawa da sauran kasashe kan yadda za a magance cutar numfashi da ta bulla a kasar
2020-01-29 16:11:44        cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya bayyana kudirin kasarsa na tattaunawa da sauran kasashe ciki har da Burtaniya, kan yadda za a tunkari batutuwan da suka shafi kandagarki da ma hana yaduwar cutar numfashi da nau'in kwayar cutar Conoravirus ke haddasawa.

Wang ya bayyana haka ne jiya Talata, yayin da ya ke tattaunawa ta wayar taro da takwaransa na kasar Burtaniya Dominic Raab.

Wang Yi wanda ila mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, ya bayyana cewa, bisa jagorancin shugaba Xi Jinping, kasar Sin ta bullo da matakan kandagarki da hana yaduwar cutar a dukkan fadin kasar, baya ga sauran matakai a dukkan fannoni dake gudana yadda ya kamata.

Ya ce, a halin da ake ciki, an yi nasarar shawo kan yaduwar cutar dama kokarin magance ta, kana kasar Sin tana da fifiko a fannin albarkatu da cimma nasarar abubuwan da ta sanya a gaba, don haka, kasar tana da karfin shawo kan wannan matsala.

Wang Yi ya ce, a matsayinta na kasar dake sauke nauyin dake bisa wuyanta, kasar Sin tana kula da 'yan kasa da baki 'yan kasashen waje dai-dai wa daida, kuma za ta ci gaba da kare lafiya da ma rayuwar kowa da kowa dake cikin kasar.

A nasa bangare, Dominic Raab, ya yaba da managartan matakan da gwamnatin kasar Sin take dauka game da wannan cuta, Ya kuma bayyana kudirin kasarsa na karfafa tsare-tsare da hadin gwiwa da kasar Sin, za kuma ta yi iya bakin kokarinta na samarwa kasar Sin kayayyakin lafiya da ake bukata don ganin bayan wannan annoba. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China