![]() |
|
2020-02-15 16:12:14 cri |
Taron ya kuma yi nuni da cewa, ya kamata a zurfafa gyare-gyaren kasuwanci, kuma a inganta bude kofa ga kasashen ketare, sa'an nan a samu ci gaba ta fannin muhimman gyare-gyare.
Baya ga haka, shugaba Xi Jinping ya kuma jaddada cewa, cutar numfashi da kwayar cutar corona ke haddasawa ta kasance wata babbar jarrabawa ga kasar Sin a fannin tsarin gudanar da harkokinta da ma kwarewarta. Ya ce, dangane da matsalolin da aka gano a wannan karo, ya kamata a inganta tsarin kandagarkin cututtuka da ma tsarin tinkarar al'amuran lafiya na ba zata na kasar.
Ya kuma yi nuni da cewa, ya kamata kasar Sin ta gaggauta bullo da dokokin tsaron halittu, tare da gaggauta kafa tsarin dokokin.
Har ila yau, ya ce ya kamata a sanya tsaron halittu cikin tsarin tsaro na kasar, ta yadda za a kyautata kwarewar kasar wajen kula da tsaron halittu.(Lubabatu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China