![]() |
|
2020-02-09 21:01:36 cri |
A cikin sakonsa, Xi Jinping ya jaddada cewa, yanzu dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka na cikin wani lokaci mafi kyau a tarihi. Bisa yanayin sauye-sauye da duniya ke ciki, karfafa gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya a tsakanin Sin da Afirka na dacewa da moriyar bai daya ta jama'ar bangarorin biyu. Kasar Sin zata ci gaba da tabbatar da nasarorin da aka cimma a gun taron kolin na dandalin tattaunawar hadin kai a tsakanin Sin da Afirka da aka shirya a Beijing a dukkan fannoni, da kuma gaggauta raya shawarar "Ziri daya da hanya daya" a tsakaninsu, don kara bada gudummowa wajen bunkasa da farfado da Afirka, da kara samar da alheri ga jama'ar sassan biyu. (Bilkisu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China