Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya jagoranci taron shawo kan cutar coronavirus
2020-02-12 21:14:08        cri
Babban sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban kasar Xi Jinping, ya jagoranci taron da ya gudana a Larabar nan, game da matakan kandagarki da shawo kan cutar numfashi, wadda kwayar cutar coronavirus ko COVID-19 ke haddasawa.

Yayin taron na yau, Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi, wanda a cikin sa ya ce a yanzu haka, an fara samun sauyi game da yanayin yaduwar wannan annoba, sakamakon aiki tukuru da ake yi, da kuma matakan kandagarki, da na shawo kan cutar da ke kara haifar da kyakkyawan sakamako.

Shugaban na Sin ya ce, matakan da ake dauka sun kai wani mataki da ke bukatar kara zage damtse, don haka akwai bukatar dora muhimmanci kan ginshikan cimma nasara, ba tare da yin kasa a gwiwa ba.

Shugaba Xi ya kara da yin kira ga kwamitocin jam'iyya, da jami'an gwamnatoci a dukkanin matakai, da su tabbatar sun sauke nauyin dake wuyan su, na cimma nasarar yakin da ake yi da wannan annoba, da kuma burin da kasar ta sa a gaba, na cimma nasarorin tattalin arziki da bunkasa zamantakewa, wadanda aka tsara a shekarar nan ta bana. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China