Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya ce Sin na da tabbacin samun cikakkiyar nasarar yakin da take yi da coronavirus
2020-02-10 21:17:54        cri
Shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin koli na JKS Xi Jinping, ya ce kasar sa na da tabbacin samun cikakkiyar nasarar yakin da take yi da cutar numfashi da kwayar cutar coronavirus ke haddasawa.

Shugaba Xi ya ce yanzu haka, ana cikin wani yanayi mai tsanani, amma kuma daukacin jami'an JKS, da rundunar sojojin kasar, da al'ummar kasar da suka hada da dukkanin kabilun ta, na tare da al'ummar lardin Hubei da na birnin Wuhan.

Xi, wanda kuma shi ne shugaban hukumar gudanarwar rundunar sojojin kasar Sin, ya yi wannan tsokaci ne, yayin da yake duba yadda ake gudanar da ayyukan kandagarki da dakile cutar a nan birnin Beijing.

Cutar numfashi ta coronavirus dai ta fara bulla ne a birnin Wuhan fadar mulkin lardin Hubei, kafin kuma ta yadu zuwa sauran sassa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China