![]() |
|
2020-02-11 16:38:18 cri |
A cikin mako guda kadai, shugaba Xi Jinping ya aika da sakwanni 2 zuwa kasashen Afirka. Kyakkyawar mu'amala a tsakanin kasashen Sin da Afirka ta nuna cewa, Sin da Afirka suna cikin mataki mai kyau wajen raya huldar da ke tsakaninsu. Yadda Sin da Afirka suke himmantuwa wajen raya al'umma mai kyakkyawar makoma ya kara nuna dankon zumuncin da ke tsakaninsu a kowa ne irin mawuyacin hali.
A farkon shekarar 2020, annobar cutar numfashi ta barke a kasar Sin, wasu shugabannin kasashen Afirka da jama'ar kasashen, ciki had da shugaban Senegal sun nuna goyon bayansu ga kasar Sin wajen yaki da annobar ta hanyoyi daban daban. A ranar 9 ga wata, a yayin taron kolin shugabannin kungiyar AU karo na 33, mahalarta taron sun bayyana goyon bayansu ga kasar Sin. Haka kuma kwamitin zartaswa na AU ya ba da wata sanarwa, inda ministocin harkokin wajen kasashen Afirka, mambobin kungiyar suka mara baya ga kokarin da gwamnati da jama'ar kasar Sin suke yi wajen dakile yaduwar annobar, sun kuma nuna tabbaci da imani kan kwarewar Sin wajen yaki da annobar.
Annoba na dan wani lokaci ne, amma zumunci yana nan daram. Kamar yadda Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a ranar 10 ga wata a yayin taron manema labaru, kasar Sin ta yi imani da cewa, bayan ganin bayan barkewar annobar, dankon zumunci a tsakanin kasashen Sin da Afirka zai kara kyautata, kana al'umma mai kyakkyawar makoma tsakanin Sin da Afirka za ta kara bunkasa.(Tasallah Yuan)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China