![]() |
|
2020-02-07 13:46:02 cri |
Yayin tattaunawar ta su, Xi Jinping ya jaddada cewa, bayan bullar cutar numfashi a kasar Sin, gwamnati da al'ummar kasar, dukkansu sun dukufa wajen yaki da cutar. Ya ce, "Mun yi kira ga dukkanin al'ummomin kasar Sin, su shimfida ayyukan yaki da cutar bisa dukkan fannoni, da aiwatar da ayyukan cikin sauri, da kuma daukar matakai masu tsanani, domin yin kandagarki, da hana yaduwar cutar numfashi a kasar Sin."
Ya ce, "A yanzu haka, mun cimma wasu nasarori, kuma Sin tana da imanin cimma nasarar wannan yaki. Kana, matsalar ba za ta hana bunkasuwar tattalin arzikin kasar a nan gaba ba."
A nasa bangare kuwa, Donald Trump ya ce, kasar Amurka tana goyon bayan kasar Sin, wajen yaki da cutar numfashi, tana kuma fatan aika masana zuwa kasar Sin, da kuma samarwa mata taimako a wasu fannoni.
Kasar Sin ta kafa asibitocin musamman cikin gajeran lokaci, lamarin da ya nuna kwarewar ta wajen tsara ayyuka, da fuskantar harkokin gaggawa. Shi ya sa, kasar Amurka ke da imanin cewa, tabbas Sin za ta ci gaba da raya tattalin arzikinta.
Haka kuma, shugabannin biyu sun tattauna game da yarjejeniyar tattalin arziki da cinikayya, ta matakin farko da kasashen biyu suka kulla, inda suka cimma matsayi daya kan ci gaba da raya dangantakar dake tsakanin sassan biyu. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China