Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Me ya sa ake ta yada jita-jita kan kasar Sin?
2020-02-14 21:47:20        cri

Bisa namijin kokarin da al'ummar Sinawa suka yi, hakarsu ta cimma ruwa ta fannin shawo kan cutar numfashi da kwayar cutar corona ke haddasawa. A jiya Alhamis, ban da lardin Hubei da cutar ta fi kamari, karuwar mutanen da suka kamu da cutar sun kai 267 a sauran sassan babban yankin kasar, wato kwanaki 10 a jere ana samun raguwar adadin.

Sai da a lokacin da labarin ya ba al'ummar kasa da kasa kwarin gwiwa, jita-jita ta fara yaduwa.

 

 

A kwanan nan, jaridar "New York Times" ta wallafa wani bayani mai taken "SARS da murar tsuntsaye da ma cutar corona: me ya sa cututtuka masu yaduwa da dama suka barke a kasar Sin?" Labarin ya ruwaito maganar Peter Navarro, shugaban kwamitin harkokin cinikayya na kasar Amurka, inda har ya bayyana kasar Sin a matsayin "na'urar renon cututtuka".

To, in dai kamar yadda labarin ya fada hakan ne, me ya sa murar da ake kira "spanish flu" da ta hallaka mutane miliyan 50 a farkon karnin da ya gabata ta fara bulla a wani sansanin soja da ke jihar Kansas ta kasar Amurka? Sai kuma a shekarar 2009, murar tsuntsaye nau'in H1N1 ta barke a kasar Amurka, har ta yadu zuwa kasashe da shiyyoyi 214, wadda daga baya ta harbi mutane miliyan 60 a fadin duniya, kuma dubu 300 daga cikinsu sun mutu. A bara kuma, murar da ake kira influenza B ta bulla a sassa da dama na kasar Amurka, har ma rahoton da cibiyar kandagarki da dakile cututtuka ta kasar Amurka ta ba da ya nuna cewa, kawo yanzu, a kalla mutane sama da miliyan 22 sun kamu da cutar, daga cikinsu kuma dubu 12 sun mutu.

 

 

Cututtuka makiya ne ga 'yan Adam baki daya, kuma babu wata kasa ko wata al'ummar da za ta iya tsira daga gare su.

A yayin da kasashen duniya ke ta kara dunkulewa da juna, da zarar kasar Sin ta shawo kan cutar, lalle harkokin cinikayya da zirga-zirga duk za su farfado a duniya baki daya, kuma hasarorin da cutar za ta haifar ga kasashen duniya za su ragu. Nasarar kasar Sin nasara ce ga duniya baki daya.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China