Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata a kawar da ra'ayin siyasa na zargin tsarin kasar Sin
2020-02-06 16:39:46        cri

A halin yanzu, Sin tana kokarin yin amfani da fifikon tsarinta, don hadin kai wajen magancewa, da yaki da cutar numfashi. Babban direktan hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa, tsarin kasar Sin, da matakan kasar suna da amfani sosai, har ba a taba ganin irinsu ba a tarihi.

Amma a hannu guda, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo, ya zargi jam'iyyar kwaminis ta Sin, da tsarin kasar Sin da kawo barazana a wannan lokaci.

Yayin da kasar Sin take kokarin magancewa, da yaki da cutar numfashi da ta bulla a kasar, a matsayin babban jami'in harkokin wajen babbar kasa a duniya, Pompeo ya bayar da wannan ra'ayi maras tushe, wanda ya sabawa manufar jin kai, kana ya kawo cikas ga Sin da Amurka wajen tinkarar kalubale tare ta hanya hadin gwiwa.

A halin yanzu, yanayin magancewa, da yaki da cutar numfashi yana da tsanani. Bisa fifikon tsarin kasar Sin, da kokarin dukkan jama'ar kasar, Sin tana da imani, da karfi wajen cimma nasarar yaki da cutar. Bayan da aka daidaita wannan matsala, tilas ne kuma Sin ta kara samun ci gaba, kana fifikon tsarin kasar zai kara taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da samun bunkasuwa a duniya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China