Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rashin dattaku na Amurka ya illata hadin gwiwar kasa da kasa game a yaki da cutar corona virus
2020-02-05 17:22:12        cri

A halin da ake ciki, kasar Sin na kara azama wajen yaki da cutar numfashi ta coronavirus da ta barke a sassan kasar, a gabar da kasashen duniya da dama ke samar da tallafi, da goyon bayan su ga kasar ta Sin.

Sai dai kuma a bangare guda, Amurka a matsayin ta na kasa dake kan gaba wajen kwarewa a fannin kiwon lafiya, a maimakon ba da tata gudunmawa, sai ta buge da janye jami'an ta dake karamin ofishin jakadancin ta na birnin Wuhan. Kaza lika ta kasance ta farko da ta sanya tsauraran matakan shigar Sinawa kasar ta, matakin da ya haifar da fargaba, da jefa razani a zukatan al'umma, wanda hakan ya zamo mummunan misali.

Kasar Sin na kallon wannan mataki na Amurka, a matsayin kaucewa sauke nauyin dake kan Amurkar na hadin gwiwar kasa da kasa, wanda ba zai taimakawa yunkurin tunkarar wannan annoba yadda ya kamata ba.

Ko shakka babu, yaki da wannan cuta ba na kasar Sin ne kadai ba. Tallafi da kuma goyon bayan dukkanin sassan kasashen duniya, zai karfafa gwiwar Sin, wajen kawo karshen wannan annoba. Kaza lika a wannan karni da duniya ke dunkulewa, kuma bil Adama ke kokarin cimma makoma ta bai daya, taimakon sauran sassan duniya tamkar taimakawa kai ne. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China