Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta yi kokarin ganin ta cimma burin bunkasuwarta a wannan shekara
2020-02-13 20:21:27        cri

Barkewar cutar numfashi da kwayar cutar coronavirus ke haddasawa ba zato ba tsammani a kasar Sin, ta kasance tamkar jarrabawa ce ga kasar, wadda kuma ta ba duniya damuwa kan cewa, ko kasar tana iya shawo kan cutar?

 

 

A jiya Laraba a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya shugabanci taron zaunannen kwamitin hukumar siyasa na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar, inda aka yi nazari kan yanayin da ake ciki, na kandagarkin cutar, da ma matakan da za a dauka don shawo kan ta. Taron da ya kasance na uku da manyan jagororin kasar Sin suka gudanar cikin kwanaki 19 da suka gabata.

Taron ya kuma isar da wasu muhimman sakwanni biyu, wato "An samu kyakkyawan sauyin yanayin da ake ciki, kuma matakan da aka dauka sun fara amfani", kuma "ya kamata a yi kokarin bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma a yayin da ake kokarin dakile cutar".

 

 

Sakwannin suna karfafawa al'ummar Sinawa kwarin gwiwa, haka kuma kwarin gwiwa ne ga duniya baki daya. Kasancewarta kasa mai karfin tattalin arziki ta biyu a duniya, kasar Sin ta ba da gudummawar da ta kai kaso 30% ga ci gaban tattalin arzikin duniya cikin shekaru da dama. A sabili da haka, bunkasar kasar Sin, na amfanar duniya baki daya.

Illolin da cutar ka iya haifarwa ga ci gaban tattalin arziki da zaman al'umma sun dogara ne ga yadda ake gudanar da ayyukan kandagarki, da dakile cutar. Yanzu haka, matakan da aka dauka sun fara amfani, wadanda suka taimaka wa kasar wajen cimma burin ci gabanta a wannan shekara.

 

 

A waje daya kuma, karin kamfanonin kasar sun farfado da ayyukansu. Abin lura kuma shi ne, taron ya kuma jaddada cewa, ya kamata a tallafawa kamfanonin da ke gudanar da cinikin waje, ta yadda za su gaggauta farfado da ayyukansu, sa'an nan a aiwatar da dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa yadda ya kamata, tare da kyautata yanayin zuba jari ga baki 'yan kasuwa, don kare moriyarsu. Matakin dai ya shaida cewa, kasar Sin na kokarin shawo kan cutar, ba ma kawai don kare al'ummarta kadai ba, har ma don kare moriyar kasa da kasa. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China