Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na karfafa niyyarta da matakanta na dakile cutar coronavirus
2020-02-11 21:33:47        cri

 

A jiya Litinin, babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis na kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban kasar, Mr. Xi Jinping, ya ziyarci wasu sassan birnin Beijing, don duba yadda ake gudanar da ayyukan kandagarki da dakile yaduwar cutar numfashi da kwayar cutar coronavirus ke haddasawa, inda kuma ya jaddada cewa, har yanzu ana fuskantar yanayi mai tsanani, kuma ya kamata a karfafa niyyar dakile cutar, tare da kara daukar tsauraran matakai, sa'an nan a dogara ga al'umma, ta yadda za a shawo kan cutar.

Wannan dai karo na uku ne da shugaban kasar Sin ya bayar da jawabi dangane da aikin kandagarki da dakile cutar. Kafin wannan kuma, sau biyu ne ya shugabanci taron zaunannen kwamitin hukumar siyasa ta kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis mai mulki a kasar, inda ya gabatar da muhimman jawabai tare da tsara ayyukan da za a gudanar.

 

 

A hakika, tun bayan barkewar cutar, a karkashin jagorancin shugaban, da ma tawagar ba da jagoranci ga ayyukan dakile cutar, an sa kaimin dukkanin al'ummar kasar, kuma sannu a hankali ne aka fara cimma nasarorin aikin dakile cutar a sakamakon ingancin tsarin kasar Sin wanda ke mai da al'umma a gaban komai tare da hada karfin kowa.

Kididdigar da hukumar lafiya ta kasar Sin ta bayar ta nuna cewa, a jiya Litinin, karuwar wadanda suka harbu da cutar ya kai 381 a sassan kasar Sin, ban da lardin Hubei da cutar ta fara bulla, wato ke nan, kwanaki bakwai a jere, ana samun raguwar adadin. Ko a lardin Hubei ma, an fara samun sauki. A sa'i daya kuma, yawan wadanda suka warke daga cutar sun karu daga kaso 1.3% zuwa 8.2%, lamarin da ya shaida ingancin matakan da kasar Sin ta dauka, wanda kuma ya karfafa gwiwar al'umma. A kwanan baya, masanin al'amuran ba zata na WHO Mike Ryan, ya bayyana cewa, yanzu da wuya a yi hasashen makomar lamarin, sai dai yadda aka fara samun sauki a lardin Hubei bishara ce, wadda ka iya shaida cewa, matakan da aka dauka sun fara amfani.

 

 

Babban sakataren MDD António Guterres, shi ma a nasa bangaren ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi namijin kokari ta bangaren kandagarki da dakile yaduwar cutar, lamarin da ya cancanci yabo. A yayin da ake kan wani muhimmin mataki na kandagarki da shawo kan cutar, yadda shugaba Xi Jinping ya duba ayyukan da ake gudanar tare da daukar muhimman matakai, karin kokari ne da kasar Sin take yi, wajen kare lafiyar al'ummarta, da ta duniya baki daya.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China