Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Yaki Da Annoba Bisa Doka
2020-02-08 20:50:12        cri

Babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar Xi Jinping ya jagoranci taro na 3 na kwamitin kula da aikin aiwatar da mulki bisa doka na kasar Sin a 'yan kwanakin baya, inda ya jadada cewa, a wannan lokaci mai muhimmanci da ake kokarin dakile bazuwar cutar Corona, ya kamata a kara nacewa ga manufar aiwatar da matakan dakile cuta bisa doka. Sa'an nan a tsaurara matakai daga fannonin kafa doka, da kula da harkokin shari'a, gami da bin doka. Furucin shugaban ya nuna ra'ayin aiwatar da mulki bisa doka, wanda jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin dake jan ragamar mulkin kasar ke tsayawa a kai sosai. Wannan umarnin da shugaba Xi ya gabatar zai sa a kara kokarin hana yaduwar cuta, da daidaita al'amura bisa doka, don tabbatar da ganin a gudanar da aikin dakile cuta yadda ake bukata.

Kiyaye doka shi ne ginshikin duk wata al'umma, kuma babbar hanya ce da ake bi don kyautata fasahar mulki. Yanzu haka, ana cikin wani yanayi mai muhimmanci a kokarin dakile yaduwar cutar Corona a kasar Sin, don haka gudanar da ayyuka bisa kimiyya da kuma doka yana da muhimmanci matuka. Kasar Sin za ta mai da wannan yakin da ake yi da annoba ya zama wata damar kyautata dabararta a fannin mulki bisa doka, ta yadda za ta samar da wani cikakken tsarin dokoki na tinkarar annoba mai amfani, da sanya kowa ya tuna da dokoki yayin da ake kokarin dakile cutar. Ta wannan hanya za a sanya kasar ta samu karin kwarewa a fannin tinkarar kalubale, da baiwa nagartaccen tsarin mulkin kasar damar taimakawa kyautata aikin mulki, ta yadda za a tabbatar da ci gaban tattalin arzikin da zamantakewar al'ummar kasar mai dorewa cikin dogon lokaci mai zuwa. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China