Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta samu karin kudaden shiga a 2019 matakin dake nuni da karfin jawo jarin waje na kasar
2020-02-14 21:01:04        cri
Wasu alkaluma sun nuna cewa, kasar Sin ta samu karin kudaden shiga a shekarar 2019 da ta gabata, sakamakon karuwar bukatun hajojinta daga ketare, matakin da ya haifar da raguwar gibin cinikayya a fannin samar da hidimomi, tare da tarin jarin waje da ya shiga kasar.

Ya zuwa karshen shekarar ta bara, karin da aka samu a wannan fanni ya kai dalar Amurka biliyan 177.5, kamar dai yadda alkaluman hukumar lura da musayar kudaden waje ta kasar ko SAFE a takaice ta fitar a Jumma'ar nan.

Darajar cinikayyar karin hajojin kasar ta daga zuwa dala biliyan 462.8, yayin da kuma gibin cinikayyar da ya shafi hidimomi ya yi kasa zuwa dala biliyan 261.4.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, kudaden jarin waje da kasar ta samu sun kai matsayin koli na dala biliyan 59.1, yayin da harkokin zuba jari a hada hadar hannayen jarin kasar, suka samu karin darajar dala biliyan 60.

A cewar kwararriya a fannin tattalin arziki, kuma mai magana da yawun hukumar SAFE Wang Chunying, daidaituwar biyan kudaden kasuwannin duniya na Sin, ya ci gaba da kasancewa a matsakaicin yanayi, inda kudaden hada hadar tsallaken kasar ke gudana yadda ya kamata. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China