Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na shawarwari da WHO a kan tawagar hadin gwiwar masanan sassan biyu
2020-02-13 20:37:03        cri
A yau Alhamis, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Geng Shuang, ya tabbatar da cewa, yanzu haka sassan masu ruwa da tsaki na kasar Sin, na shawarwari tare da tawagar hukumar lafiya ta duniya (WHO), dangane da ayyukan da tawagar bincike ta hadin gwiwar masanan sassan biyu za ta gudanar.

Geng Shuang ya ce, mukasudin tawagar bincike ta hadin gwiwar masanan sassan biyu shi ne, masanan su yi musayar ra'ayoyi a kan halin da ake ciki, da ma aikin da aka gudanar na kandagarkin cutar numfashi, da kwayoyin cutar coronavirus ke haddasawa, ta yadda za a samar da shawarwari ga kasar Sin, da ma sauran kasashen duniya da cutar ta shafa, don daukar matakai na gaba. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China