Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na goyon bayan kamfanonin cinikin waje da su dawo ayyuka
2020-02-13 12:34:54        cri
Taron da zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya gudanar a jiya Laraba, ya bayyana cewa, yayin da ake karfafa aikin kandagarki da hana yaduwar cutar numfashi, a sa'i daya kuma, kasar Sin tana goyon bayan kokarin da kamfanonin cinikin ketare suke yi na dawo wa bakin aikin, da kara taimakon kudin cinikayya, da amfani da inshorar fitar da hajoji yadda ya kamata. Haka kuma, kasar Sin tana fatan kamfanonin za su shiga hadin gwiwar kasa da kasa, kana gwamnatin Sin za ta samar da yanayi mai kyau wajen raya cinikin ketare.

Haka kuma taron ya bayyana cewa, ya kamata a gaggauta kaddamar da manyan shirye-shiryen dake shafar jarin waje, da aiwatar da dokokin jarin waje yadda ya kamata, da kyautata yanayi ga masu zuba jari daga ketare, da kuma kiyaye ikon kamfanoni masu jarin waje yadda ya kamata.

A sa'i daya kuma, an ce, ya kamata a habaka bukatun al'ummomin Sin. Da mai da hankali kan muhimman batutuwa, da kyautata aikin takardun lamuni na gwamnatocin wuraren kasar, da gudanar da aikin zuba jari bisa hasashen da kwamitin tsakiya ya yi, da sa kaimi ga al'ummar kasa da su zuba jari, da kuma ciyar da wasu manyan shiye-shirye gaba. Haka kuma, ya kamata a kyautata ayyukan ba da hidima domin inganta bukatun al'ummar kasa a fannin yin sayayya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China