Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kofar kasar Sin a bude take ga Amurka wajen aiwatar da hadin gwiwar tinkarar cutar corona
2020-02-14 19:49:25        cri
A yau Juma'a, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, tun bayan barkewar cutar numfashi da kwayar cutar corona ke haddasawa, kullum kofar kasar Sin a bude take ga Amurka, wajen aiwatar da hadin gwiwa. Kasar Sin za ta ci gaba da hada kan kasa da kasa, ciki har da Amurka wajen tinkarar cutar, da kiyaye lafiyar al'ummar duniya.

Wasu rahotanni sun nuna cewa, a kwanan baya, shugaban kwamitin kula da harkokin tattalin arzikin kasar Amurka karkashin fadar White House Larry Kudlow, ya bayyana cewa, Amurka ta yi bakin cikin rashin gayyatar ta, don ta sa hannu, a aikin shawo kan cutar corona, da kuma yadda kasar Sin ta yi rufa-rufa kan halin da ake ciki. Game da wannan batu, a gun taron manema labarai da aka shirya ta yanar gizo, Mr. Geng Shuang ya ce, tun bayan barkewar cutar, kasar Sin na bin ka'idar bayyana halin da ake ciki yadda ya kamata, da kuma kare lafiyar al'ummar duniya, tana kuma hada kai da kasa da kasa wajen dakile cutar.

Geng Shuang ya yi nuni da cewa, sassan kiwon lafiya na kasashen Sin da Amurka, na tuntubar juna kan manufofin da ake aiwatarwa, suna kuma yin musayar bayana game da cutar kan lokaci. Kasar Sin na maraba da masanan kasa da kasa, ciki har da masanan Amurka, da su shiga tawagar bincike ta hadin gwiwar masanan kasar Sin da WHO. Baya ga haka, sau da dama shugaba Donald Trump na Amurka, da kuma ministan kiwon lafiya na kasar Alex Azar, sun jinjina wa kasar Sin, kan yadda take bayyana halin da ake ciki ba tare da rufa rufa ba. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China