Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen BRICS sun sanar da goyon bayansu ga Sin wajen yaki da cutar numfashi
2020-02-12 16:27:10        cri
Jiya Talata, kasar Rasha ta fidda sanarwar shugaba a madadin kungiyar kasashen BRICS, don nuna goyon baya ga kasar Sin wajen yaki da cutar numfashi da kasar ke fama da ita. Sa'an nan, a yau Laraba, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana cewa, sanarwar da kasashen BRICS suka fidda ta nuna akidar kasashen BRICS na goyon bayan juna a lokacin da daya ke fuskantar matsaloli, ta kuma nuna goyon bayan da gamayyar kasa da kasa suka nunawa kasar Sin wajen yaki da wannan cuta. Kasar Sin tana yabowa matuka dangane da wannan lamari.

Haka kuma, Geng Shuang ya ce, dukkanin mambobin kasashen BRICS kasashe ne da tattalin arzikin ke saurin bunkasa, kana kasashe masu tasowa, kuma muhimman abokan kasar Sin. Kasar Sin tana son ci gaba da yin hadin gwiwa da gamayyar kasa da kasa, ciki hada da kasashen BRICS, domin yaki da wannan annoba domin tabbatar da kiwon lafiyar yankin da ma kasashen duniya baki daya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China