2020-01-31 15:48:48 cri |
A ranar 28 ga watan Janairu ne, shugaba Donald Trump na Amurka, ya sanar da wani shirin samar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, don goyon bayan mamayen matsugunan Palasdinawa da Isra'ila ke yi. Abubuwan da ke kushe cikin shirin dai, sun goyi bayan Isra'ila, da watsi da bukatun Palasdinawa, matakin da ya kara fuskantar rashin amincewa tsakanin galibin mazauna yankin gabas ta tsakiya, ciki har da Palasdinawa.
A jiya ne kuma, Palasdinawa da dama suka shirya gangami a wajen birnin Ramallah dake yammacin kogin Jordan don nuna rashin amincewarsu da shirin da Amurkar ta gabatar.
A wannan rana kuma, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya tattauna da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a Moscow, domin jin ra'ayinsa game da shirin da shugaba Trump din ya gabatar. A halin yanzu dai, bangaren Rasha, bai fitar da wata sanarwa game da ganawar bangarorin biyu ba.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China