Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Somalia ta bayyana goyon bayanta ga kasar Sin wajen yaki da annobar cutar numfashi
2020-02-06 19:03:37        cri

Ministan harkokin wajen kasar Somalia Ahmed Isse Awad ya bayyana goyon bayan gwamnatin Somalia ga gwamnatin kasar Sin wajen yaki da annobar cutar numfashi. Ministan ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da jakadan kasar Sin a Somalia Qin Jian a kwanan baya.

Ya kuma nuna cewa, Somalia ta dauki matakan yin rigakafi a filin jiragen saman kasar, kamar binciken yanayin zafin jikin fasinjoji. Ya kara da cewa, yanzu 'yan Somalia 50 da ke zaune a birnin Wuhan da annobar ta bulla suna cikin koshin lafiya. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China