Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masana sun bukaci Afirka ta Kudu da ta magance dalilan dake haddasa hare-haren da ake kaiwa baki a kasar
2019-09-18 09:09:51        cri
Wasu masana sun bayyana cewa, kamata ya yi Afirka ta Kudu ta hada kai da takwarorinta na Afirka, don magance abubuwan dake haddasa hare-haren kin jinin baki a kasar daga tushe.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua game da lamarin, mai sharhi kan harkokin siyasa dake jami'ar Afirka ta Kudu, Somadado Fikeni, ya ce, bai kamata a kau da kai ga batun karancin albarkatu a cikin al'ummu matalauta ba, sannan ya kamata gwamnati ta gano bakin zaren warware wannan matsala.

Bayan da shugaba Cyril Ramaphosa na kasar Afirka ta Kudu ya aika manzanni na musamman zuwa kasashen Najeriya, da Senegal da Ghana, da Tanzaniya, da Zambia, don ba su hakuri kan hare-haren da suka shafi 'yan kasashensu, Minista a fadar shugaban kasar Afirka ta Kudu Jackson Mthembu, ya yarda cewa, wajibi a magance dalilan dake haddasa nuna kyama ga baki mazauna kasar. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China