Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan tattalin arzikin Afirka ta Kudu daga watan Afrilu zuwa Yuni ya karu da kashi 3.1 cikin dari
2019-09-04 13:52:07        cri
Alkaluman kididdigar da hukumar kididdiga ta kasar Afirka ta Kudu ta fitar a jiya sun nuna cewa, karfin tattalin arzikin Afirka ta Kudu daga watan Afrilu zuwa Yuni ya karu da kashi 3.1 cikin dari bisa makamancin lokacin bara, wanda ya zarce hasashen da aka yi.

Shugaban sashen nazarin tattalin arziki da cinikayya na jami'ar Witwatersrand ta kasar Afirka ta Kudu Jannie Rossouw ya bayyana cewa, wannan karuwa ta shaida kyakkyawar alama, wadda ta kawar da mummunan tasirin da koma bayan tattalin arzikin kasar ya haifar a farkon watanni 3 na bana, da kuma magance yiwuwar koma bayan tattalin arzikin kasar. Ya ce, wannan ya shaida cewa, yanayin bunkasuwar tattalin arzikin kasar ya dawo bisa turba. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China